Jarumar shirin Izzar so Khadija ta bayyana wani boyayyan sirri akan harkar Fim data tsinci kan ta a ciki
Ficacciyar Jarumar shirin nan mai dogon zango Izzar so wato Khadijah Yobe ta bayyana yadda harkar Fim ta sauya mata rayuwar ta cikin dan kankanin lokaci.
A lokacin da Jaruma Khadijah take tattuawa da wakilin Jaridar Damukaradiyya akan yadda harkar Fim ta sauya mata rayuwar ta, ta bayyana cewa.
Cikin dan kankanin lokaci rayuwa ta ta dauya tun daga lokacin dana fara bayyana a cikin shirin Izzar so duk da cewa ba shi ne Fim din dana fara fitowa a ciki ba.
Inda ta kara da cewa: Amma shirin Izzar so shi ne ya daga darajar ta Mutane suka sanni sosai har na zama abar alfahari a cikin Mutane, wannan yasa lokaci guda rayuwa ta ta sauya.
Jaruma Khadijah taci gaba da cewa: Sauyin rayuwa da na samu yasa Mutane da dama sun sanni sannan nima kuma nasan Mutane sosai inda hakan yasa na zama tauraruwa wanda ake son gani a duk inda naje.
Don haka babu abin da zan ce da Allah sai dai godiya kuma ina fatan Allah ya kara daukaka ni a harkar Fim na kai inda ma bana zaton zan kai, domin ko halin da nake ciki ma a yanzu na sami kai na ne ba tare da nadan zan kai ba.
Daga karshe Jaruma Khadijah ta roki Allah yasa ta gama harkar Fim lafiya, domin a rinka tunawa da ita sabida gudunmawar da ta bada.