Makiya cigaban Jihar Kano ne kadai suke adawa da Gwamna Abdullahi Ganduje, cewar Indabawa Aliyu Imam
Makiya Ci Gaban Jihar Kano Ne Kadai Suke Adawa Da Gwamna Ganduje. Daga Indabawa Aliyu Imam.
A cire batun adawa ko siyasa a dubi gaskiya Jihar Kano bata taba samun Gwamnan da yayi aiki kamar Abdullahi Umar Ganduje ba, Mutum ko makiyin Ganduje ne ya san da wannan sai dai kawai ya bi son zuciyar sa.
Saboda jahilci na mutane sai ka ji suna caccakar Gwamna Ganduje wai yana yanka masallaci da makabarta ana yin shaguna, to a ba ni nassi guda da ya ce kar a yi shago a masallaci ko ma’kabarta, a tsarin shari’ar musulunci komai halal ne sai abin da nassi ya haramta kamar yadda Malaman usulul fiqhi ke cewa.
Duba da haka ke nan gina shago da masallaci ba zai zama haram ba tun da har a sami dalilin haramta shi ba Kuma gine—ginen Shagunan Maigirma Gwamna Ganduje yana yin su ne ‘Sadaqatul jariya’ wanda ko bayan ransa zai cigaba da samun lada.
Shagunan da ake ginawa a masallatai ana yin haka ne don masallaci ya tsaya da kafarsa a dinga samun kudin man janareto da sauran bukatun masallaci ba sai an yi roko ba, haka ma’kabartu ana yi ne don samun kudin siyan tukunya da ‘kasar rufe ‘kabari.
Gina shaguna a makabartu suna da muhimmanci matuka
yana dakile batagari wanda ke zuwa su ciri sassan jikin mamaci a kabari.
Haka naga wani bidiyon Kwankwaso yana cin zarafin Maigirma Gwamnan Kano Ganduje yana tsine masa don kawai an yi shaguna a masallacin idi, ba zan yi mamaki
ba Kwankwaso da kansa ya san ba shi da ilmin addini kuma mabiyan sa ma sun sani furucin jahili daban yake dana mai ilmi.
Duk irin cikar da jama’a zasu yi ha a cika ko rabin masallacin Idi ga shi kuma a tsakiyar kasuwanni masallacin yake, ke nan mene aibu don an yi shaguna ta gefen masallacin don a raya Jihar Kano a samar da kasuwanci wanda zai rage marasa aikin yi a Kano.
Shi Kwankwaso da yake wannan magana filaye nawa ya yanka ya siyar, duk irin aika- aika da babakeren daya aikata har yana da bakin da zai soki Ganduje.
Mu al’ummar Jigar Kano muna goyon bayan shirin Gwamba Ganduje na bunkasa Jihar Kano Filayen jikin badala duka a gine su, Rafukan da suka tashi daga gadon kaya har kofar nassarawa a cike su a yanka filayen a yi gine-gine domin cigaban Jihar Kano.
Baba Ganduje dattijon arziki Allah ya cigaba da taimakon ka wajen hidimtawa jama’ar Jihar Kano da kuma addinin Musulinci.