Jaruma Hadiza Gabon tana sami addu’o’i da fatan nasara a rayuwar ta ga Al’umma kan taimakon da tayiwa Sani Garba SK da kuma gidan Marayu
Kamar yadda kuka sani Hadiza Gabon Jaruma ce a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood wanda ta jima a Masana’antar ana damawa da ita.
Jaruma Hadiza Gabon tayi kaurin suna wajan tallafawa marasa karfi da kuma marayu wanda basu da Iyaye, wanda har ma ake kiran ta da uwar marayu.
A duk lokacin da Jaruma Hadiza Gabon ta sami labarin wani na kusa da ita kama daga abokan sana’arta da abokan arziki, takan taimaka musu iya gwargwado ga abin da suke bukatar a taimaka musu kama daga kayan abin ci kudi da dai sauran su.
Iban baku manta ba a kwanakin baya Jaruma Hadiza Gabon ta bada tallafin kayan abin ci ga gidan marayu wanda a lokacin ta sami karin daukaka da kuma addu’o’i daga wajan Al’umma, da Allah ya kara daukaka ta ya cika mata burin ta na alkairi Duniya da Lashira.
Bayan wannan lokacin Jarumin Masana’antar Kannywood Sani Garba SK wanda abokin aikin ta ne ya kwanta jinyar da yake fama da ita, wanda har neman taimakon al’umma ake domin a sami kudin da za’a cigaba da daukar dawaiyiyar sa akan jinyar da yake fama da ita.
Bayan labarin naiman taimakon ya karade kafafan sada zumunta inda Jama’a suka yi ta yi masa addu’ar Allah ya ba shi lafiya, sannan kuma nan take aka fara samin Mutanen da suka taimaka masa.
A lokacin ne Jaruma Hadiza Gabon taji wannan labarin naiman taimakon da Jarumi Sani Garba SK yake, nan da nan ba tare da bata lokaci Jarumar ta taimaka masa da zunzurutun Kudade har Naira dubu dari biyu da hamsin 250K, domin neman lafiyar sa.
Inda a wannan lokacin ma Jama’a suka rinka yiwa Jaruma Hadiza Gabon addu’a kala-kala da kuma fatan Allah yasa rayuwar ta tayi albarka, duk wani buri nata wanda take nema Duniya da Lashira Allah ya cika mata su.
Wanda har kawo yanzu Jarumar tana samin addu’o’i daga gidan marayun da ta taimakawa da duk ma wanda ta taimaka masa a rayuwar sa.