Mutuwar Aure na da Sani Musa Danja baya nufin mun zama abokan gaba ba kamar yadda wasu suke zato domin shi din uban ‘Yaya na ne, cewar Mansurah Isah
Kamar yadda kuka sani Tsohuwar Jarumar Masana’antar Kannywood Mansurah Isah ta kasance Mata ga Jarumi kuma Mawaki Sani Musa Danja, inda a wannan karon ta bayyana wani al’amari game da mutuwar Auren su.
Mansurah Isah take cewa: Mutuwar Aure na da Sani Musa Danja ba wai yana nufin mun zama abokan gaba ba, inda ta bayyana hakan a lokacin da suke tattaunawa da DLC Hausa ta Daily Turust.
Tsohuwar Jarumar ta kara da cewa: Ban ga wani abin aibu da don Auren mu ya mutu domin Sani shi ne uban ‘Yayana, kuma dama abokina na ne bayan haka kuma abokin aiki na.
Mansurah Isah ta kara da cewa: Don haka ban ga wani dalili da yada Jama’a suke ta yawan maganganu akan hakan ba a yanzu haka muna cikin Duniyar Zamani, kasancewar ya sake ni ba yana nufin mun zama makiya ba.
Bayan rabuwar Auren Mansurah Isah da Sani Musa Danja Jama’a da dama sun yi mamaki ganin yadda suka bayyana a cikin wani sabon Fim mai suna Fanan, wanda Mansurah Isah ta shirya shi.
Wanda a lokacin da aka gan su waje daya Jama’a suke tunanin ko Sani Musa Danja ya mayar da Mansurah Isah gidan sa, duba da yadda aka sun cigaba mu’amalar su kamar yadda suka saba.