Raddi ga Daliban Abduljabbar da suke murnar mutuwar Malam Mas’ud Hotoro daya daga cikin Malaman da suka yi mukabala da Abduljabbar
Raddi ga Daliban Abduljabbar da suke murnar mutuwar Malam Mas’ud Hotoro wanda yana daya daga cikin Malamn da suka yi mukabala da Abduljabbar.
Mum sami labarin mutuwar mutum daya daga cikin hudu da sukayi mukabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wato Malam Mas’ud Hotoro, wanda ya kasan ce tsohon Dalibin Anduljabbar din inda muka sami labarin Malamin yayi hatsarin Mota akan hanyar Kaduna zuwa Zariya.
Sai dai wani abin al’ajabi yayin da ake alhinin rasuwar Malamin su kuma wasu daga cikin Daliban Abduljabbar suna wallafa labarai da cewa, ga irin ta nan dake nuna jayayya sa Malamin da son ganin an kashe shi.
Malamin nasu bai mutu ba gashi nan shi ya mutu da dauran zantuttuka dake nuna kamar mutuwar ta shi wata nasara ce a gare su.
Daya daga cikin Malaman da suka yi Makabalar Sheikh Kabiru Bashir kofar wambai wansa ake masa lakabi da hayaki fidda na kogo, yayi martani ga Daliban Abduljabbar din a wani dogon runutu da ya kwafo daga dan uwa Awaisu al’arabi fagge inda ya wallafa a shafin sa da cewa.
Rasuwar Malam Mas’ud Hotoro Allah maji rokon bayin sa, mun wani gari da wani labari mai sosa rai na rasuwar Malam Mas’ud Hotoro, daya daga cikin dakarun da suka baya Manzon Alla S.A.W kariya a ranar fadan karshe tsakanun al’ummar Musumai da Abduljabbar.
Tabbas duk mai rai sai ya dandana Mutuwa kuma abin da Allah ya bayar nasa ne kuma wanda ya karba ma nasa ne, muna rokon Allah mai rahama mai jin kai yajikan Malam Mas’ud ya yi masa rahama ya gafarta zunuban sa ya kyautata makwancin da.
Domin kuji cikekken labari sai ku kalli bidiyon dake kasa.