Advertising
Advertising
Labarai

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Ekiti tare data Jihar Jigawa sun bayyana Danzago a matsayin shugaban APC a Jihar Kano

Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi da takwaransa na Jigawa wato Abubakar Badaru, sun kira Ahmadu Haruna Zago da shugaban jam’iyar APC a Jihar Kano.

Advertising

Zago wanda a ka fi sani da Ɗanzago shine shugaban APC, tsagin Sanata Ibrahim Shekarau dake Jihar Kano.

Da alama dai za’a iya cewa ta faru ta ƙare a shugabancin APC bayan da Fayemi wanda shine Shugaban Muryar Gwamnonin Nijeriya tare da Badaru, su ka kira Danzago da shugaban jam’iyar APC a Kano.

A ‘Yan watannin jam’iya mai mulki a Jihar Kano ke fuskantar rikici wanda yaki ci yaki cinyewa inda ya haifar da rabuwar jam’iyar zuwa bangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da na tsohon gwamna Sanatan Kano ta Tsakiya wato Shekarau.

Advertising

Tun a lokacin zaben shugabannin jam’iya na Jiha aka samu rabuwar Jam’iyyar APC gida biyu, inda bangaren Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba shi kuma tsagin Shekarau ya zabi Danzago.

Sai dai kuma a ranar Talata da ta gabata wata babbar kotu dake Abuja ta rushe shugabacin Abdullahi Abbas ta kuma tabbatar da na Danzago a jihar, duk da cewa tsagin Gandujen sun bayyana cewa za su daukaka kara.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa: gwamnonin a yau Asabar yayin jawabin su a wajen taron cikar shekarar Cibiyar Bincike kan Dimokradiyya ta Aminu Kano dake karkashin Jami’ar Bayero shekaru 21, kowannen su ya kira Danzago da shugaban jam’iyar APC a yayin shimfida a jawaban su.

Jaridar ta ƙara da cewa: Wannan shine karo na farko da aka ambata Danzago a matsayin shugaban APC a bainar jama’a, tun bayan da a ka yi zaben Shugabannin jam’iyar a Jihar Kano.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button