Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Daraktan shirin Kwana Casa’in Salisu T Balarabe ya bayyana dalilin da yasa suka sauya Salma daga cikin shirin

Salisu T Balarabe wanda shi ne Daraktan shirin nan mai dogon zango Kwana Casa’in ya bayyana dalilin da yasa aka sauya Jarumar cikin shirin wato Salma.

Advertising

A wata shira da Salisu T Balarabe yayi da BBC Hausa ya bayyana cewa, ita da kanta Salman ta bayyana cewa baza ta cigaba da fitowa a shirin ba.

Sannan ya kara da cewa: A tsarin mu na shirin Kwana Casa’in a duk lokacin da za’a gabatar da wani zango akan sanar da Jarumai kafin lokacin da cewa, an yanke lokacin da za’a dauki wannan zangon.

Amma wasu daga cikin Jaruman suna bayyana cewa, bazasu sami damar yin wannan zangon ba sabida yanayi na karatu ko kuma wani dalilin su na daban.

Advertising

Ya kara da cewa: Lokacin da muka tuntubi Salma akan cewa zamu dauki shirin Kwana Casa’in zango na shida 6 sai ta sanar da mu cewa gaskiya bazata sami dama ba.

Amma sai muka bukaci jin dalilin da yasa ta fadi haka inda ta sanar da mu cewa, hakan yana da nasaba da Mahaifanta ne wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa ba.

Domin kuji cikekkiyar shirar da BBC Hausa tayi da Daraktan shirin Kwana Cada’in Salisu T Balarabe akan sauya Salma daga cikin shirin, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button