Duk wanda yake shaye-shaye domin ya gusar da hankalin sa to tabba sai ya dandana azaba a ranar Lashira, cewar Dr Bashir Aliyu
Babban limamin Masallacin Juma’a na Alfurqan dake Jihar Kano “Dakta Bashir Aliyu” ya bayyana cewa, shaye-shayen miyagun kwayoyi yana sanyawa ayi wa mai amfami da su azaba a ranar lahira.
Inda Malamin yake bayyana cewa: A Musulunci Allah Ya haramta shan kayan maye kuma Ya yi hani ga cinikin su, domin a wannan zamani da muke ciki zakuga har da masu dakon kwayoyin sa maye daga wata Jihar su kai wata.
Sannan ya kara da cewa: Shan miyagun kwayoyi na gusar da hankali da lafiyar jikin dan Adam domin duk wanda yake amfani da wadan nan kwayoyin sa mayen, to tabba idan kuka rula da shi zakuga bashi da cikekken hankali.
Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake hudubar sallar Juma’a a masallacin Alfurqan dake Alu Avenue a Jihar Kano a ranar Juma’a.
Malamin ya yi kira ga hukumomi da su tashi tsaye wajen yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin alumma.
A cewar Malamin: Jihar Kano da Kaduna da kuma Katsina suna cikin manyan Jihohin da ake samun rahoton shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran dangin kayan maye.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin Jihohi da kuma Hukumar hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi wato “NDLEA” da su tashi tsaye wajen kawar da kayan maye a tsakanin alumma.