Labaran Kannywood

Kalli yadda Jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik tare da Iyalan sa suna shakatawa a bakin Ruwan Tekun Legos cikin farin ciki

Kamar yadda kuka sani yawancin Jaruman Kannywood Maza suna fita da Iyalan su wajan shakatawa domin kara dankon soyayya a tsakanin su, inda wasu ma suke barin Kasar gaba daya su tafi izuwa wata Kasar domin shakatawar inda wani lokacin zakuga ana sako su a bakin ruwa.

To a yau ma mun sami wata bidiyo wanda Tashar Tsakar Gida dake kan manhajar Youtube ta wallafa inda muka ga Jarumin Masana’antar Kannywood Sadik Sani Sadik, tare da Iyalan sa suna shakatawa a bakin Ruwa a Legos.

Yadda zaku ga a cikin bidiyon Jarumin suna shakatawa tare da Iyalan nasa a bakin Ruwan cikin farin ciki da jin dadi, inda har ma aka dauki zafafan hotunan sua wajan.

Domin ku kalli yadda Jarumi Sadik Sani Sadik yake shakatawa tare da Iyalan sa a bakin Ruwan Tekun Legos, sai ku kalli bidiyon da muka ajiye a kada.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button