Advertising
Advertising
Labarai

Tunda Shugaba Buhari ya yaudare mu yaci amanar mu to za’a yi bala’i tare da ni kuma za’a yi zanga-zanga, Sheikh Bello Yabo Sokoto

Ficaccan Malamin addinin Mulunci Sheikh Bello Yabo dake Jihar Sokoto ya bayyana cewa: Shugaban Kasa Muhammad Buhari shi da kan sa yasan cewa yaci amanar al’ummar Kasar Nageriya ba sai an fada masa ba.

Advertising

Sannan ya kara da cewa: Shugaba Muhammad Buhari ya zo ya shafawa al’ummar Nageriya mai ga dadin baki ashe amanar al’ummar zai ci, inda Sheikh Bello Yabo ya sake fadin cewa an yi ikirarin cewa za’a kashe shi kuma a kan shi yafi sau nawa.

Bayan haka Sheikh Bello Yabo yace: Akwai Mutanen da suka mutu a kan shi wanda kuma shi yasan da hakan amma ko yaje ya yiwa Iyalan su gaisuwa, sannan Sheikh Bello Yabo yayi addu’a da cewa tun da anci amanar su Allah ya isar mana.

Malam yace: Indai akan ankai lita mai ₦65 aka fito zanga zango idan aka kai shi ₦340 dole mufito ayita da mu koda za’a yi kashe kashe.

Advertising

Domin kuji cikekken bayani daga bakin Sheikh Bello Yabo akan wannan raddi da yake yiwa shugaba Muhammad Buhari, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

https://youtu.be/OwEja6a76Q4

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button