Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an asibitin Dala ta Kano sun kama matashin da yayi basaja a matsayin majinyaci ya sace wayar marasa lafiya

Jami'an asibitin Dala ta Kano sun kama matashin da yayi basaja a matsayin majinyaci ya sace wayar marasa lafiya

Kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa suka ruwaito cewa, an kama matashin da ya yi basaja ya sace wayar masu jinya a asibitin kashi ta jihar Kano.

Advertising

Dubun matashi mai suna Abdul’aziz ta cika, bayan da ya daura bandeji a kafarsa kamar ya ji rauni, ya shiga cikin marasa lafiya ya sace musu waya.

Lamarin ya faru ne a Babban Asibitin Kashi na Dala a jihar Kano, a jiya Juma’a, bayan da jami’an tsaron asibitin suka cafke shi ya dauke wa wani majiyyaci wayar salula.

Daya da ga cikin jami’an tsaron asibitin mai suna Ismail Ismail ya bayyana cewa, ya ga matashin yana ta zirga zirga ne sai jikin sa ya bashi cewa matashin bashi da gaskiya.

Advertising

Inda yake cewa, da naga yana ta zirga zirga sai ban ce masa komai ba, sai nasa masa ido ina ganin motsinsa, na san dai a asibitin nan marasa lafiya ba sa zirga zirga irin haka.

Sau uku yana wuce wa ta inda na ke duty can sai na ga ya shiga wani daki bai dade da shiga ba, sai na ji an saka ihun barawo sai kuwa na gan shi ya fito a guje sai na bishi da ni da sauran abokan aiki na.

Muna zuwa wani lungu da ya shige sai muka tarar har ya cire rigarsa, shine muka damke shi, in ji Ismail.

A cewar Abdul’aziz, ya yi basaja ne domin ya
samu kudin motar komawa garin su sannan kuma yace, shi wannan bandejin ba na karya ba ne sabida dama a kwai rauni a kafarsa shine
ya daura shi.

Bayan Abdul’aziz ya amsa laifin sa ya roki ayi
masa afuwa, Jami’an tsaron asibitin sun ce zasu mika shi ga ‘yan sanda da zarar sun kammala bincike.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button