Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mawaki Abdul D One yaron Umar M Shareef zai Angonce da zazzafar Amaryar sa mai suna Umma Salma Sulaiman

Mawaki Abdul D One yaron Umar M Shareef yana shirye shiryen zama sabon Ango.

Advertising

Ficaccan matashin Mawakin Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa Abdulkadir Muhammad wanda aka fi sani da Abdul D One yana gaf da zama sabon Ango.

Wannan dai yayi dai-dai da abin da Hausawa suke da cewa, abu namu maganin a kwabe mu domin kuwa dan cikin Masana’antar Kannywood kuma Mawaki yana shirin zama angancewa.

Abdul D One dai matashin Mawaki ne wanda aka san shi tare da Umar M Shareef, domin a lokacin da tauraruwar sa ta fara haskawa wasu ma basa iya tantance muryar sa data mai gidan nasa Umar M Shareef, domin kuwa muryar tasu tana kama sosai.

Advertising

To a yanzu dai Mawaki Abdul D One lokaci yayi amma bana mutuwa ba domin Mawakin zai angwance ne tare da dalleliyar Amaryar sa mai suna, Umma Salma Sulaiman, wanda ake mata lakabi da Salma Fresh.

Sannan kuma cikin Amincewar Allah za’a sha wannan kasaicaccan bikin a ranar 12 ga wannan watan da muke ciki na Desemba.

Domin kuji cikekken labari akan Auren Mawaki Abdul D One wanda yake yaro ga Umar M Shareef, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin kulla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button