Kalli sabon Kamfanin da Ali Artwork ya bude na saida Motoci da Gidaje a Jihar Kaduna da Abuja domin samar da aikin yi ga Matasa
Ficaccan dan wasan barkwancin nan na Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood Ali Muhammad Idris wanda aka fi sanin sa da Ali ArtWork, ya bude wani katafaren kamfanin sai da Motoci da cinikin Gidaje.
Ali Artwoek ya gina katafaren Kamfanin nada ne a Jihar Kaduna da kuma babban birnin tarayya Abuja mai suna Aliartwork Enterprises.
Dan wadan barkwancin na Masana’antar Kannywood ya bude wannan Kamfanin ne domin samar da aiyukan yi ga Matasa, sannan shima zai raba kafa ne domin Hausawa suna cewa sana’a goma maganin mai gasa.
Ana gudanar da abubuwa da dama a wannan saban Kamfamin da Ali Artwork ya samar, kamar sayar da Motoci da kuma bayar da su haya, sau kuma hada-hadar sayar da Gidaje da Filaye da kuma farkokin tuntuba.
A shafinsa na Facebook, Ali Artwork ya wallafa wasu daga cikin hotunan buɗe wajen, inda ya gayyaci ƴan uwa da abokan arziki domin su ta ya shi murna.
Sannan kuma munga Jarumin ya wallafa hoton saban Kamfanin nasa wanda ya dube shi a Jihar Kaduna da kuma babban birnin tarayya Abuja, a shafin sa na sada zumunta Instagram.