Advertising
Advertising
Labarai

Kotu ta yankewa wani Saurayi hukuncin biyan tarar naira Miliyan biyu da dubu dari shida 2.6M akan yaudarar Budurwar sa da yayi tsawon shekara 7

Wata kotun majistare dake Kumo a karamar hukumar Akko a Jihar Gombe ta yankewa wani Matashi hukuncin biyan tarar naira Miliyan biyu da dubu dari shida 2.6M, sakamakon yaudarar Budurwar sa da yayi har tsawon shekaru bakwai 7.

Advertising

Da farko Budurwar ita ta fara yin karar Saurayin nata a Kotu domin abi mata hakkinta inda ta bayyana Kotun cewa, sun shafe tsawon shekaru bakwai suna soyayya amma sai taji labarin cewa zai auri wata ba ita ba.

Nan da nan Alkalin Kotun ya umarci Saurayin Budurwar da ya biya tarar wannan zunzurutun kudaden naira Miliyan biyu da dubu dari shida 2.6M, ko kuma ya auri Budurwar idan ba haka kuma za’a tura shi gidan gyaran hali na tsawon shekaru takwas 8.

Inda Saurayin ya zabi ya fada auren wacce aka sanya musu rana da ita domin zai auri tsohuwar Budurwar sa da ya yaudare ta, sabida gudun hukuncin da Alkalin Kotun ya yanke masa.

Advertising

Daga: Yushau Garba Shanga.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button