Mai hali bazai fasa ba: kalli wata bidiyo da Jaruma maryam Yahaya ta saki wanda ta maida ta gidan jiya
Kamar yadda kuka sani Maryam Yahaya Ficacciyar Jaruma ce a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood, wanda ta dauki lambobin yabo tare da samin daukaka a wajan Masoyan ta da Jama’a masu kallon shirin Fim din Hausa.
Idan baku manta ba Jaruma Maryam Yahaya ta kwanta rashin lafiya a kwanakin baya wanda taki ci taki cinyewa da kowa yake tunanin asiri aka yi mata, inda har aka fara cece-kuce da maganganu kala-kala akan rashin lafiyar Jarumar.
Amma zuwa yanzu Allah ya baiwa Jarumar lafiya da har take samin damar wallafa hotunan ta tare da bidiyo yin ta a shafin ta na sada zumunta Isragram, amma duk da haka kowa yaga jaruman zai gaskata ta kwanta rashin lafiya mai tsanani duba da ramewar da tayi.
A yau kuma mun sami wata bidiyon Jaruma Maryam Yahaya wanda Tashar “Hausapro Tv” dake kan manhajar Youtube ta wallafa, inda muka ga Jaruma tana wasu abunuwa da suka janyo mata cece-kuce wanda a lokacin da ta wallafa bidiyon kan ta ko dan kwali babu.
Wanda dama Jarumar tun kafin ta kwanta rashin lafiya ta saba wallafa irin wadan nan bidiyoyin a shafin ta na sada zumunta Instagram, sannan a yanzu ma bayan ta sami lafiya ta dora daga inda ta tsaya dama Hausawa suna cewa mai hali bazai fasa ba.
Zaki iya kallon bidiyon dake kasa domin ku kalli abin da Jaruma Maryam Yahaya take a cikin bidiyon, tare da karin bayani akan ta tun lokacin data kwanta rashin lafiya har kawo yanzu data sami sauki ta koma bakin aiki, wato taci gaba da wallafa hotunan ta tare da bidiyoyi kamar yadda ta saba.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.