Labaran Kannywood

Ya kamata Maza suna dukan Matan su idan suka musu laifi, cewar Naziru Sarkin Waka

Kamar yadda kuka sani Naziru M Ahmad wanda aka fi sanin sa da Sarkin Waka Ficaccan Mawaki ne a Masana’antar Kannywood wanda ya shahara sannan kuma ya sami daukaka a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

Naziru Sarkin waka ya wallafa wata bidiyo a shafin sa na sada zumunta Intagram da yake bayani a ciki kan cewa, yan da kyau Maza suna dukan matan su idan suka musu laigi.

Inda wannan furucin nasa ya janyo cece-kuce da maganganu a shafin nasa inda wasu suke kalubalantar sa kan wannan furucin da yayi, inda wasu kuma suke ganin wannan maganar tasa ya fada ne kawai san ran sa.

Domin kuji cikekken bayanin da Nazir Sarkin waka yake akan duk macen da tayiwa Mijin ta lai fi ya dake ta, sai ku kalli bidiyon dake kasa sannan kuma a kasan bidiyon zakuga ra’ayoyin da Mutane suka fada akan wannan furucin da yayi.

Ga bidiyon na domin ku kalla kai tsaye kuji cikekken bayani daga bakin sa.

Teemash_food_and_catering tace: Daga baya kenan, ur post will mislead so many people Ba kaman masu son zuciya. Da daka sa sai ka bi next slide kayi fashin baki.

Adamu_dan_borno Ban jarasakallon yace: video nan nakaba Dan banda Iokaci,,,Amman natsaya A inda naji kanacewa masu jin haushi suna ta zaji,,,Rankadadi bawani magananjin haushi air,,,duk abon da kaga mun padama jiya daddari gaskiya ce,,,, dake girman kai yama yawa shinin bazaka iya pitowa kace kayi kuskuri bah.

prince.a.u.a yace: Ehhh hadisi baya gaba é daya ayar qur’ani amma fah shi wannan hadisin shike fassara kur’ani sbd wani sakon da qur’ani yakawo zakaga dunkulalle ne amma hadisi shi zai fasashi yayi bayaninsa and kuma babu wani batu na hadisi dayaci karo dana kur’ani soo take notee

fatima_abdullahi_9 tace: Sosai kowa shi inimi kogine musan mun na musulinci har in kinja islamiya hmm kin San me akenufi ai ya Allah yasamugane mukuma fahamta.

officialzeezango yace: Gaskiya ne sarki wannan haka yake kawai san zuciya ne na wasu mutanan Allah yasaka da alkairi.

captain_tera yace: Allah ya saka f, nazo nayi é? comments jiya naga comments din mutane raina ya baci na wuce. mutanen mu basa son karatu wallahi. da mas’alar boko deh ka kawo da kaji reference and citation.

bb_giwa_jr yace: Kanada matsala katsaya iya matsayin ka dan nanaye Allah ya kwantarda fituna cikin zukantan mutane babbane Zunubi ne hassala Irin wannan kabi duniya a hankali Naziru ko mai gidanka matsalarsa kenan a rayuwa yanke zance gabagadi babu tarjama Allah ya shiweka Damu Baki daya.

muhammad_mb mb yace: Jahilchi yafi hauka, @ wai mutun daga yaga yana iya yin wani kanikancin Iarabcinsa shikenan sai yake jin shi mai ilimi ne?……….kafin yin mgn
akan wadansu ka fara yi ma kanka ne, ka kawo mana ayar da tace mutum ya zama maroki.

Wadan nan sune kadan daga cikin wadan da suka yi tsokaci akan furucin da Nazir Sarkin Waka yayi kan cewa ya kamata Maza suna dukan matan su idan suka musu laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button