Yadda aka gudanar da shagalin bikin bude gidan sinima na haska Fina-Finan Duniya a kasar Saudiyya
Za’a yi shagalin bikin nuna Fina-Fina Dumiya na farko a kasar Saudiyya a birnin Jiddah, kasa da shekaru hudu 4 sannan kuma da dage haramcin haska Fina-Finai a kasar.
Wannan shagalin bikin da za’a ayi na nuna Fina-Finai a kasar ta Saudiyya za’a dauki tsawon kwanaki goma 10, inda za’a haska Fina-Finai guda dari da talatin da takwas 138 daga sannan Duniya.
Kamar yadda shafin BBC Hausa suka ruwaito cewa: Za’a karrama Darakta Mace wanda ta kasance ta farko a Saudiyya mai suna “Haifa al-Mansour”, wacce ta fara yin Fim din Wadjba sannan kuma ta lashe kyauta.
Za’a gudanar da shagalin bikin ne domin bunkasa Masana’antar Fina-Finan ta kasar Saudiyya ta fuskar nuna Fina-Finan a gidan sinima wanda aka bude tun shekarar 2018.
Ga hotunan da suka dauka nan na shagalin bikin.