Yamzu-Yanzu: ‘Yan Bindiga sun kona wata Motar fasinja tare da Mutane 42 a ciki a Jihar Sokoto
Rahotanni daga jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya ya bayyana cewa, ‘Yan Bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutane arba’in da biyu a ciki 42.
Rahotannin sun bayyana cewa: ‘Yan Bindigar sun sace fasinjojin sun inda suka fito daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar, domin yin kaura zuwa wasu yankunan Najeriya saboda ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga a inda suke.
Wasu shaidu da aka samu sun bayyanawa shafin BBC Hausa cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe tara 9 na safiyar ranar Litinin.
Motar da take dauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni tayi tafiyar da bai fi kilomita shida 6 ba zuwa kauyen Gidan Bawa, inda wannan masifa ta afka musu kamar yadda wadan da suka yi aikin ceton suka bayyana wa shafin BBC Hausa.
Shafin BBC Hausa sun yi kokarin jin ta bakin rundunar ‘Yan sandan jihar, amma hakar su ba ta cimma ruwa ba ko da suka kira kakakin rundunar ‘Yan sandan a wayar sa basu same shi ba domin wayar a kashe take.
Kazalika mun kira kwamishinan tsaro na jihar har sau uku shi ma bai dauka ba, yankin Arewa maso yammacin Najeriya na daya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya.
Sai dai a lokuta da dama gwamnatocin yankin na cewa, suna yi iya bakin kokarin su domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umarsu, amma abin da al’umar ke cewa ba sa gani a kasa.