Daraktan Kannywood Falalu a Dorayi ya yiwa Shugabanni wankin babban bargo bayan da ‘Yan ta’adda suka kashe wasu Mutane ‘Yan Jihar Sokoto
Ficaccan Jarumi kuma Darakta a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood “Falalu a Dorayi, ya wallafa wani rubutun abin alhini da takaici akan al’ummar Arewacin Nageriya da ake yawan kashe su, inda yayi jawabi a cikin runutun nada kamar haka.
Gazawar Shugabanni kullum kara bayyana take a tsakanin zababbu da wadanda aka nada don rike wasu madafai.
Abin takaici ne abin Allah wadarai Kuna zaune a gida a shigo a kashe ku, a farma iyalanku mata Kuna kan hanya a tare a debe ku a kashe na kashewa.
Ku bar gari domin gudun tsira a tare ku a kone ku Kuyi noma domin samun abinci a kone gonar da amfanin cikinta, Ko kuma kai da gonarka sai Dan ta’adda ya saka muku haraji sannan ku noma ko girbe abin da kuka Namiji.
Shugabannin Yanzu muddi datti bai hau kan rigar su ba basa gane ana guguwa a garinsu, tsakanin kisan rai da Fyade hana Kasuwanci da kone abinci a Gona, da kone Mutane da ran su duk babu wanda Gwamnatin Jiha da ta Kasa da wakilan su ba su san yana faruwa ba.
Idan kanaso kaga karfin ikon su to kaba kujerar su ko ku koma Jam’iyarsu, Allah mun tuba ka kawo mana agajin ka ya As-Samadu ka taimakemu wajan zaben nagari masu kishin mu a zabe mai zuwa. Amin.
Darakta Falau a Dorayi yayi wannan rubutu ne akan kone motar ‘Yan Jahar Sokoto da ‘Yan ta’adda suka yi, bayan sun fito da ga karamar hukumar sabon birni wani kauye mai suna gidan bawa.
Inad bayan fitowar tasu suka ci karo da ‘Yan ta’addan shi ne suka kone musu Motar da suke ciki sannan suka kashe wasu daga cikin Mutanen.