Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Bayanin Datti Assalafiy akan tsohuwar jaruma Fati Bararoji ya dauki hankulan jama’a bayan data fara tsufa a yanzu

Bayanin Datti Assalafiy akan tsohuwar jaruma Fati Bararoji ya dauki hankulan jama'a bayan data fara tsufa a yanzu

Bayanin shahararran barubuci Datti Assalafiy akan tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Fati Bararoji ya dauki hankulan jama’a, duba da yadda bayanin ya yi dai-dai da rayuwarta wanda a yanzu haka tsufa ya riske ta.

Advertising

Datti Assalafiy ya wallafa bayanin a shafin sa na sada zumunta Facebook kamar haka.

DUNIYA KENAN.

Ita ma jarumar Hausa fim Fati Bararoji tsufa ya bayyana, shafe-shafe baya boye tsufa, komai lokaci ne, idan lokacin kyauwun fuska da kyawun fata da dirin jikin ya wuce baya dawowa har abada.

Advertising

Muna rokon Allah Ya arzurtamu da kyakkawan tsufa.

Bayan dan gajeren wannan bayanin na Datti Assalafiy da ya wallafa a shafin nasa, sai kuma ya sanya hoton jarumar tare da abokanan ta inda kowa ya tabbatar da cewa, maganar Datti Assalafiy gaskiya ce domin a yanzu haka da gaske tsufa ya riski Fati Bararoji.

Da yawa daga cikin tsofaffan jaruman masana’antar kannywood Mata wanda suka yi sharafin su a shekarun baya tsufa ya fara riskar su, inda wasu ma daga cikin su suke neman Mazan da zasu aure su domin su kara sa tsufan nasu a gidajen Mazan su amma abin yaci tura.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button