Advertising
Advertising
Labarai

Turkashi: An sake sace mutun 15 a kauyen Zanfara bayan 60 din da suke hannu yan bindiga.

A ranar Alhamis Wasu gugun yan bindiga dauke da manyan makamai suka sun sace mutane 15 a kauyen Yarkatsina da ke gundumar Kekun Waje a Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara

Advertising

Wannnan harin nazuwa bayan kwanan 36 da suka wuce bayan an sace mutane 60 a yankin kuma har zuwa yanzu mutanen na tsare a hanun masu garkuwar.

Mutanen da suke zaune a yankin sun tabbatar wa da manema labarai cewar maharan sun fara da Zafafan hare hare ne bayan yan sa kai sun hanasu sakat a yankin.

Wani Mazaunin kauyen mai suna sadik, ya ce yan Yan sa-kan ne suke gadin yankin. Dalilin daya saka ’yan bindigar suka ce ba za su saki mutanen ba muddin ba su ajiye makamansu ba.

Advertising

“Bayan mutum 15din da suka sace yanzu, akwai ’yan kauyen su 76 a ke nan a hannunsu, ciki har da mata da kananan yara.

“ yan bindiga sun tsaya kai da fata akan bazasu saki wannan mutane ba matukar yan sa kai basu aje makamin suba, inda yan sakan sukace bazasu ajeba, za su cigaba da bawa kauyensu kariya inji sadik

Ya ce mutanen kauyen sun dauki darasi ne daga wasu garuruwan makwabtansu da suka ajiye makamansu bayan tattaunawa, amma duk da haka har yanzu ba a fasa kai musu hari ba.

“Wadannan ’yan bindigar ba su da imani ko kadan. Kowace irin yarjejeniya aka yi da su sai sun zo sun kawo hari, shi ya sa muka ki amincewa mu ajiye makaman,” inji shi.

Sai dai duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Mungode da irin wanan kokari da kuke, Ku cigaba da bibiyar mu dan samun zafafan labaidai.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button