Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Na shiga harkar Fim ne domin na sami daukaka Duniya ta sanni kamar yadda sauran Jarumai suka samu, cewar Jaruma Amina Sani

Kowa ce Jaruma a Masana’antar shirya Fina-Fina Hausa ta Kannywood tana shiga harkar Fim ne domin cimma wani buri nata, domin da yawa daga cikin su suna shiga harkar Fim ne domin Duniya ta san da su.

Advertising

To a wannan lokacin ma wata Jaruma kuma Mawakiya a Masana’antar Kannywood mai suna Amina Sani, ta bayyana manufar da yasa ta shiga harkar Fim.

Jaruma Amina Sani ta bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin Jaridar Damukaradiyya inda ta bayyana cewa, ta shiga harkar Fim ne domin tayi suna Duniya ta san da ita kamar yadda sauran Jaruman suka daukaka har Duniya tasan da su.

Amina Sani ta kara da cewa: Kamar yanda kowa yake da manufa ta shigar sa Fim duk wani abu da yake so ya fara to nima haka nazo da tawa manufar a wannan Masana’antar, don haka Ni dai nazo ne domin na samu daukaka na yi suna kuma Duniya ta sanni.

Advertising

Jaruma Amina tace: Kowa ya na son ya daukaka duniya ta san da shi don haka nima na fito domin na bayyana kaina a sanni Kuma na samu daukaka, don haka ne ma na shigo harkar fim Kuma Alhamdulillahi a yanzu ina ganin nasara a Kan abun da na sa a gaba.

Domin a yanzu na fito a Fina-Finai da dama Kuma na fito a wakoki masu yawa, wanda wasu ni na dauki nauyin shirya su wasu Kuma aiki ake bani nake yi.

Wakilin Jaridar Damukaradiyya ya sake tambayar Jaruma Amina Sani da cewa: Amma ke manufar ki ta bambanta da sauran Jarumai da suke cewa sun zo ne domin su fadakar ta hanyar fim ya abun yake.

Sai Amina ta fada masa cewa: To ai ka San kowa da irin tasa manufar ni Kuma tawa nake fada maka, shi yasa ma ni ban boye maka ba ko da kuwa ta bambanta da ta wasu ni iya abun da yake zuciyata Kenan.

Ta kara da cewa: Ko zaka yi fadakarwa sai ka samu daukaka mutane zasu rinka sauraron ka don haka nake so Duniya ta sanni, Kuma ina fatan nan gaba kadan burina zai cika don haka ina fatan masoya na zasu taya ni da addu’a don na samu na cimma nasarar abun da na sa a gaba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button