Advertising
Advertising
Labarai

Saudiyya ta haramtawa ‘Yan Nageriya shiga kasar ta sabida sabuwar cutar data bulla a yanzu mai suna “Omicron”

Saudiya Ta Haramta Wa Yan Najeriya Shiga Kasarta Saboda Sabuwar Cutar Omicron.

Advertising

Gwamnatin Saudi Arabiya ta bi sahun wasu kasashen duniya wajen hana jiragen sama da suka tashi daga Najeriya shiga kasar sakamakon samun wasu mutanen dake dauke da sabon nau’in cutar korona da ake kira Omicron.

Rahotanni daga birnin Kano sun ce: yanzu haka maniyata Umrah da dama sun makale a birnin sakamakon wannan mataki da Saudiyar ta dauka, yayin da jami’an kula da tashohin jiragen saman Malam Aminu Kano suka tabbatar da samun umurnin hana jirage tashi zuwa kasar.

Wata matafiya da yanzu haka take birnin Kano akan hanyar ta na zuwa Umrah a kasar ta Saudiya ta shaidawa RFI Hausa cewar tabbas an sanar da su cewar gwamnatin Saudiya ta soke tafiyar su daga Najeriya.

Advertising

Majiyar Blueink News Hausa da Jaridar Daily Trust ta jiyo ta bakin wani jami’in ofishin Jakadancin Saudiyar dake Kano na cewar tabbas sun samu umurnin hana jiragen sama daga Najeriya tafiya kasar.

Sai dai Jaridar ta ruwaito cewar: Duk da wannan umurnin, wani babban jami’in kamfanin jiragen sama ya shaida mata cewar jirage biyu sun tashi yau da safe daga Abuja
zuwa Jeddah wadanda suka hada da Qatar Air da Badar Air.

Gwamnatin Najeriya ta bakin ministan yada labarai Lai Mohammed ta bayyana bacin ran ta da irin wannan mataki da kasar Birtaniya da kuma Canada suka dauka na hana baki daga Najeriya zuwa kasar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button