Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Daraktan shirin Labarina mai dogon zango Aminu Saira ya bayyana Jarumar da zata maye wajan Laila a cikin shirin

Kamar yadda kuka sani a shirin Labarina mai dogon zango wanda Malam Aminu Saira ya shirya shi, an sami sauye sauye da dama inda harma aka cire wasu daga cikin Jaruman shirin.

Advertising

Daga cikin Jaruman da ake kokarin sauyawa a cikin shirin Labarina akwai Jaruma Laila wanda tayi aure a ‘Yan kwanakin nan, duba da auren da tayi shi tasa za’a maye wajan ta da wata sabuwar Jarumar.

To a yau kuma mun sami wata wallafa daga shafin Ficaccan Daraktan shirin Labarina Malam Aminu Saira, inda ya wallafa hoton Jaruma Fati washa tare dayin wata tambaya kan cewa idan aka sanya ta a shirin Labarina wajan wace Jaruma zata maye.

Inda Mutane suka fadin ra’ayoyin bakin su kan cewa za’a sanya Jaruma Fati washa ne a shirin domin ta maye wajan Jaruma Laila, domin kowa yana ganin tayi aure ba lallai ne ta cigaba da harkar Fim ba.

Advertising

Haka dai Mutane suka rinka ajiyewa ra’ayoyin su a sashen tsokaci inda ra’ayin nasu yake zuwa daya akan cewa Jaruma Fati washa zata maye wajan Laila ne idan aka sanya ta a cikin shirin Labarina, kuma maganar tasu akwai kamshin gaskiya a ciki kamar yadda kowa ma yake ganin hakan ne zai faru.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button