Labaran Kannywood

Duk da nayi aure bazan daina fitowa a harkar Fim ba domin ita ce sana’ata da nake samin kudi, cewar Jaruma Rahama MK

Tun bayan da Jarumar cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango Rahama MK tayi aure a watan da ya gabata Jama’a suke ta tofa albarkacin bakin su akan auren da tayi, da kuma ganin a wani matsayi take akan cigaba da shirin Fim musamman shirin Kwana Casa’in.

Amma Jaruma Rahama MK tayi shira da gidan Jaridar Damukaradiyya dake Jihar Kano inda ta tabbatar da cewa, zata cigaba da harkar Fim din musamman Kwana Casa’in da kowa yafi sanin ta a cikin shirin.

Jaruma Rahama MK ya kara bayyana cewa: Harkar fim kamar aikin Gwamnati ne ko kasuwanci da Matan aure suke yi, haka zata cigaba da yin fim tun da sana’ar ta ce da take yi kuma take samin kudi saboda auren na ba zai hana ni fitowa a fim ba.

Daga karshe Jaruma Rahama MK tayi godiya ga masoyanta da suka mata addu’ar fatan alkairi game da auren da tayi.

2 Comments

  1. Ok, I will marry u with ur conditions only if you must obey me and see me as your husband as for film I am ok by it, we can talk as mature people or call me or send me your number for better discussion

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button