Advertising
Advertising
Labarai

Duk wanda ya fito ya rantse cewa Abduljabbar ya zagi Manzon Allah S.A.W zan bashi kyautar Dalar Amurka 5K, inji wani dan kasar Ghana

An sa gasar makudan kudade ga duk wanda ya rantse cewa Sheikh Abduljabbar ya zagi Manzon Allah S.A.W.

Advertising

To har yanzu dai lamarin Sheikh Abduljabbar yana kotu inda ake cigaba da fafatawa, inda kuma wasu al’amura a gefe suke cigaba da faruwa.

Kamar yadda kuka sani an kulle Sheikh Abduljabbar ne a kurkuku bisa zargin cewa yayi kalaman batanci ga Annabi Muhammad S.A.W da kuma sahabban sa.

To a halin yanzu dai wani masoyin Sheikh Abduljabbar dan kasar Ghana mai suna Mista Fu’ad wanda yake da wani shafi a Facebook wato Qibla FM, ya kasa wata gasa mai gwabin gaske kan cewa.

Advertising

Duk wanda ya fito ya rantse kan cewa Sheikh Abduljabbar ya zagi Manzon Allah S.A.W to zai bashi kyautar Dalar Amurka har dubu biyar $5K, wanda yawan kudaden zai yi dai-dai da kusan Naira Miliyan uku 3 na Kudin Nageriya.

Domin kuji cikekken labari akan wannan gasar makudan kudaden da masoyin Sheikh Abduljabbar dan kasar Ghana ya saka kan cewa, duk wanda ya futo ya rantse cewa Abduljabbar ya zagi Manzon Allah S.A.W to zau bashi wannan kudaden, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button