Shugaba Muhammad Buhari ya isa Jihar Legos domin kaddamar da wasu ayyukan Jiragen ruwa na yaki da sauran abubuwa
Shugaban kasar Nageriya Muhammad Buhari ya ya isa Legos babban birnin kasuwanci na Nageriya domin kaddamar da wasu ayyuka a yau din nan.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa: Cikin ayyukan da shugaba Muhammad Buhari zai kaddamar a yau a Jihar Legos, har da sabbin Jiragen ruwa na yaki a tadhar ruwa ta Sojojin ruwa dake Victoria Island.
Ba tare da taba lokaci ba Hukumar kiyaye hatsura dake Jihar Legos ta “Latma” ta baiwa al’umma shawara akan su kiyaye bi titin Amhadu Bello, sakamakon ziyarar da shugaba Muhammad Buhari zai kai.
Tun Sojoji da ‘Yan Sanda da Jami’an DSS suka cika unguwar Victoria Island wanda a nan ne shugaba Muhammad Buhari zai sauka, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Bayan haka ana sa ran idan shugaba Muhammad Buhari ya kaddamar da wannan aiyyukan zai halarci kaddamar da wani Littafi wanda Chief Bisi Akande ya rubuta.