An bayyana tarihin rayuwar Tsohuwar Jaruma Fati Muhammad da abin da rayuwar ta ta kun sa.
Kamar yadda kuka sani Fati Muhammad Ficacciyar Jaruma ce a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood, an bayyana wani takaicaccan tarihin rayuwar ta da kuma gudunmawar da databar a Masana’antar Kannywood.
Majiyarmu ta samu tattara bayyanai daga sani hamza funtua dan jaridar legit takaitaccen tarihin rayuwar tsohuwar Jaruma Fati Muhammad da gudumuwarta a masana’antar kannywood.
Kamar yadda ya rubuta labarin kamar haka.
An haifi Fati Muhammad ranar 15 ga watan Yuni 1982.
Fim din @fatymuhd na farko a masana’antar shi ne “Da Babu.
Sannan kuma ga kadan daga cikin shirin Fina-Finan da tsohuwar Jaruma Fati Muhammad ta fito a Masana’antar Kannywood.
– Sangaya, Zarge, Marainiya
– Mujadala, Kudiri, Tutar So
– Garwashi, Tawakkali, Gasa
– Abadan Da’iman, Zo mu Zauna
– Tangarda, Hujja, Al’ajabi
– Halacci, Samodara, Zumunci
– Murmushin Alkawari, Gimbiya
– Bakandamiya, Taskan Rayuwa
– Nagoma, Babban Gari.