Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ana mana kisan wulakanci a Arewa ta’addanci na karuwa amma an rasa wanda zai fito yayi magana, Martanin Jaruma Gadiza Gabon

Ficacciyar Jarumar Masana’antar Kannywood Hadiza Gabon wanda ake mata lakabi da uwar marayi, ita ma ta nuna rashin jin dadin ta kan kisan gillar da akewa al’ummar Arewacin Nageriya a wannan lokacin.

Advertising

Sannan kuma Jaruma Hadiza Gabon tayi korafi akan cewa: Shugabannin Arewa sun kasa nemawa al’ummar dake zaune a Arewacin Nageriya ‘Yan cin su, kamar yadda takwarorin su ‘Yan Kudu suke fafutukar nemawa al’ummar su ‘Yan ci da zaman lafiya.

Wannan yawan korafe korafen yana faruwa ne lokacin da Jama’a da dama suke yawan nuna alhinin su akan kisan wulakancin da akewa al’ummar Arewa, da kuma rashin tsaron da yayi tsamari a Arewacin Nageriya.

Jaruma Hadiza Gabon tayi nuni da wani yaro da aka kashe a Kudancin Nageriya a Jihar Legos, inda Jama’a yankin suka fito suna zanga-zanga wanda har shubaga Buhari yaje yayi musu alkawarin za’a yi cikekken bincike.

Advertising
https://www.instagram.com/adizatou/p/CXON1FirrZQ/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button