Bayyanar tarihin rayuwar Jarumin Kannywood Abdul M Shareef Jama’a sun yi mamakin yadda yake
Kamar yadda kuka sani Abdul M Shafeef Ficaccan Jarumi ne a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood, wanda yake fitowa a cikin shirin nan mai dogon zango wato “WUFF!!” wanda Mawaki Lilin Baba ya shirya shi.
A yau kuma mun sami labarin takaicaccan tarihin rayuwar Jarumi Abdul M Shareef, da kuma gudun mawar da ya bada a Masana’anyar shirya Fina-Finai ta Kannywood.
Ga dai cikekken labarin tarihin rayuwar Jarumi Abdul M Shareef.
Jarumi Abdul’aziz Mohammed Shareef ya cika shekaru 36 a duniya.
A shekarar 2012 @abdulmshareef ya ajiye sana’ar waƙa, ya koma harkar fina finai gadan gadan, inda ya shiga da ƙafar dama, domin ya shahara cikin karamin lokaci.
Ya fito a cikin fina finai da dama, amma wanda ya fara haska shi shine fim din Makashinta wanda @tijjaniasase_real ya shirya.
Sannan kuma ga kadan daga cikin shirye-shiryen da Jarumi Abdul M Shareef ya fito.
Da Ace Babu Zuciya, Wuff
Karshen Mujadala, Makashinta
Yar Agadez, Dattijo, Ali Baba
Gamu Nan Dai, Bana Bakwai
Hawaye Na, Ba Zan Barki Ba
Garwashi, Kaddara, Jani-Muje
Rayuwarmu, da sauransu.
Bayan haka Jarumi Abdul M Shareef yana da ‘Yan uwa biyu wanda suma a cikin wannan masana’antar ta Kannywood suke, Umar m Shareef da kuma Mustapha M Shareef.
Sannan kuma Jaruma Abdul M Shareef yayi aure wanda har ma Allah ya albarkace su da haihuwar ‘Yaya hudu 4, Maza uku 3 da kuma Mace daya 1.