Labaran Kannywood

Jarumi Adam a Zango tare da Jaruma Zee Preety sun yi maganganu cikin bacin rai kan wasu Mutane 42 da aka kone

Kamar yadda kuka sani a wannan lokacin yawancin Jarukan Kannywood suka korafi akan mutanen da aka hada su waje daya a cikin mota aka banka musu wuta, wanda hakan ya kara janyowa shugabanni maganganu kala-kala.

To a yau ma Jarumi Adam a Zango tare da Jaruma Zee Preety sun yi maganganu cikin bacin rai akan yadda ake kashe al’ummar da basu ji basu gani ba, kamar yadda aka yiwa wasu daga cikin Jama’ar Jihar Sokoto inda aka kuna Mutane 42.

Bayan maganganun da Jarumi Adam a Zango yayi cikin bacin rai, ita ma Jaruma Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zee Preety tayi maganganu sosai cikin bacin rai.

Domin kuni maganganun da Jaruman suka yi akan wannan abu da yake faruwa a yanzu na rashin imani da ‘Yan ta’adda suke aikatawa Jama’a, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kai tsaye.

https://youtu.be/WsjsXVZp1es

Sannna kuma ku kalli wannan bidiyon dake kasa wanda a ciki ne Jaruma Zulaihat Ibrahim wato Zee Preety tayi maganganun ta cikin bacin rai kan abubuwan da suke faruwa a yanzu na rashin imani.

https://youtu.be/EnkHBzOLkJI

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button