Advertising
Advertising
Labarai

Mawakin Abdul D One yayi zazzafan martani ga shugaba Buhari akan nuna halin ko in kula kan kisan gillar da akewa Mutane

Kamar yadda kuka sani a ‘Yan kwanakin nan ana yawan kashewa Mutane musamman Mutanen da suke Arewacin Nageriya, inda ake musu kisan wulakanci wanda a yanzu haka ake tsaka da maganganu akan Mutane 42 da aka kone su a Jihar Sokoto.

Advertising

Shugaban Kasa Muhammad Buhari yana yawan shan maganganu daban-daban akan wannan abin dake faruwa a Arewacin Nageriya, inda Jama’a suke magana kan cewa yayi shiru tare da nuna halin ko in kula akan lamarin.

Inda a wannan lokacin Jaruman Masana’antar Kannywood suke yawan martani akan wannan ta’addancin da yake faruwa a Arewacin Nageriya, wanda a halin yanzu za’a yake shawarar fitowa zanga-zanga domin Jama’a su nuna cewa sun gaji da ta’addancin da yake faruwa.

Wanda a yanzu haka Mawakin Masana’antar Kannywood Abdul d one yayi magana mai zafi kan shugaban kasa Muhammad Buhari, inda ya nuna cewa daman shi burinsa a duniya ya aurar da ‘Yayan sa.

Advertising

Mawakin ya kara da cewa: Dama tunda ya samu ya aurar da su shine munka zamo wulakantattu a wajen sa ga abinda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Instagram.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button