Yanzu-Yanzu wani al’amari ya bayyana akan ta’addanci da kisan rashin imanin da ake wa al’ummar Arewa
Hakika al’amura sun yi muni a arewaci Najeriya ta yadda ‘Yan Bindiga suke kashe Mutane basu ji ba basu gani ba,
Hakika al’amura suna cikin wani hali a Najeriya komai ya tabarbare babu wani mai hankali da zai musanta hakan, tun hawan wannan gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari har yanzu babu inda ake kashe
mutane irin arewa.
Tabbas akwai rashin imani irin yadda bata gari ke bude wuta kan fararen hulla da jami’an tsaro musamman a arewacin Najeriya, abu ne mai matukar tada hankali da
kada zuciya.
Tabbas labarin mummunan harin da aka kaiwa wasu Mutane akan hanyar su ta zuwa neman abin ci inda aka kashe Mutane 42, hakan ya zama abin takaici matuka.
Ina mika sakon ta’aziyya ga al’ummar jihar Sokoto da kuma gwamanati jihar, da kuma iyalan wadanda abin ya rutsa dasu.
Muna kara jaddada kira ga jami’an tsaro da gwamnatin Najeriya, da su kara zage dantse domin shawo kan wannan matsalar tsaro, a arewacin Najeriya, dama kasa baki daya.
Sannan ina jaddada kira ga al’umma su rika taimakawa hukumomin tsaro da muhimman bayanai domin katse yunkurin yan ta’adda.