Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe wani kwamishina a jihar Katsina dake Arewacin Nageriya
Yan bindiga sun kashe kwamishina a Katsina.
Rahotanni daga Jihar Katsina dake Arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa, ‘Yan Bndiga sun kashe wani Kwamishinan ‘Yan Sanda na Juhar inda suka tabbatar da faruwar lamarin a wani taron manema labarai da daddare.
Kwamishinan ‘Yan Sandan yace: Tuni an fara bincike kan mutuwar kwamishinan kimiyya da fasaha na Jihar ta Katsinan, don haka babu wani dogon bayani da zan iya yi yanzu, sai dai a saurara sai binciken ya yi nisa, a cewar shi.
Ya kara da cewa: Tuni aka kai gawar mamacin asibiti sannan kuma bayanai sun tabbatar da cewa an kashe Kwamishina “Dr Rabe Nasir” a gidansa dake rukunin gidaje na Fatima Shema Estate a cikin birnin Katsina.
Rahotanni daga Jihar Katsina dake Arewacin Najeriya na cewa: ‘Yan Bindiga sun kashe wani kwamshina a Jihar Katsina dake Arewacin Najeriya, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar ya tabbatar da lamarin a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, inda wasu rahotanni sun tabbatar da lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare.
Kwamishinan ‘Yan Sanda yace: Tuni an fara bincike kan mutuwar kwamishinan kmiyya da fasaha na jihar Katsinan, don haka babu wani dogon bayani da zan iya yi yanzu, sai dai a saurara sai binciken ya yi nisa..