Advertising
Advertising
Uncategory

Zamu fito muyi zanga-zanga mukai korafi har fadar shugaban Kasa akan kisan wulakancin da akewa ‘Yan Arewa, cewar Zainab Bint Hijazi

Zainab Ahmad wacce aka fi sani da Bint Hijazi ta fito ta bugu kirji inda take bayyana cewa: zata jagoranci zanga-zanga a yau Juma’a 12 ga watan Disambar shekarar 2021 , a babban birnin tarayya Abuja kan kisan kiyashin da ake yiwa al’ummar Arewa amma gwamnati tana nuna halin ko in kula.

Advertising

A wata hira da tayi da fitaccen dan jaridar nan ma’aikacin gidan jaridar DW “Nasiru Adamu El-HikayaEl” Zainab ta bayyana bacin ranta a fili inda take cewa, tunda taga cewa abin ba na kare bane ya kamata ta sadaukar da rayuwarta domin ceto al’ummar Arewa.

Zainab Bint Hijazi ta kara da cewa: Abinda ta kasa ganewa shine, ‘Yan Arewa an mayar da su bayi ne ko kuwa rayukan su ba’a dauke su a bakin komai bane, inda tace yadda ake kashe mutane a Arewa ko kaji ba’a yiwa irin wannan kisan wulakancin.

Zainab tace: Wannan abu da yake faruwa a Arewa babu wanda yake fitowa yayi magana daga ‘yan jarida, Malamai, ‘yan siyasa da sauran su, duka babu wanda yake magana akan wannan abu da yake faruwa.

Advertising

Amma Zainab Bint Hijazi ta bayyana cewa: Malam Bello Yabo ya nuna zai goyi bayanta wajen gabatar da wannan zanga-zanga, inda tace ya bayyana cewa zai fito wannan zanga-zanga da za’a gabatar a yau.

Kamar yadda Jaridar Labarunhausa na ruwaito cewa: Zainab tace a yau Juma’ar nan za su fita kuma zasu gindayawa gwamnati bukatu, inda ta ce a cikin bukatun zasu nemi gwamnati ta tura sojojin sama dana kasa suje inda wadannan mutane suke tunda an riga an san inda suke a cikin Dajukan.

Ta kara da cewa: Babu maganar ace yau anje an kashe ‘Yan Bndiga a nan gobe a wancan wurin inda tace suna so ayi wannan abu a cikin ‘Yan kwanaki a gama kowa ya huta domin kuwa wulakancin da ake yiwa al’umma ya yi yawa.

Zainab tace: Har wani bidiyo aka aika mata inda aka nuno gonaki ana watsa musu fetir ana banka musu wuta, inda tace hakan alamu ne kawai dake nuni da cewa ana so a karar da yankin Arewa.

Ta ce tabbas akwai wani abu a kasa, ana so ne kawai a karar da yankin Arewa ya zama ‘yan Arewa sun koma kame-kame na wajen da za su zauna.

Ta kara da cewa: Wannan zanga-zanga da za’a yi ba’a ware kowa ba inda tace zanga-zanga ce da ta shafi duk wani mutum dan Arewa kuma mai kishin Arewa, tafiya ce da ta shafi duk wani wanda yake ganin yana cikin kunci a yankin Arewa tafiya ce ta kowa da kowa babu wanda aka ware a ciki.

Sannan Zainab tace: A kowacce Jiha akwai shugabanni da suka nuna goyon baya wajen wannan zanga-zanga saboda haka kowa zai dauki jama’ar shi zasu bayyana inda za su hadu.

Inda tace: A bangaren ta kuma a birnin Abuja a yau da misalin karfe 8 na safe zasu fito. Zainab tace ita ta dauki wannan abu a matsayin jihadi dan haka bata damu ba idan har sun fito sun kashe su ko sun kama su.

Ta kara da cewa: zasu fara tafiyar daga Unity Fountain inda zasu dangana har zuwa fadar shugaban kasa, domin kai masa kukan halin da yankin Arewa ke ciki.

A karshe Zainab ta yi kira ga ‘yan jaridu na gida Najeriya dama na kasashen ketare da su fito su bada goyon baya don tabbatar da cewa sun dauki duk wani abu da ake yi a wajen wannan zanga-zanga, inda ta ce zanga-zanga ce ta lumana, don haka baza a bari wani ya tada hankali ko ya jawo abinda zai zama matsala ba a wajen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button