Advertising
Advertising
Labarai

Allah ya isa tsakanin mu da Buhari: zazzafan martanin Audu Bulama Bukarti ga shubaga Buhari game da abin dake faruwa a yanzu

Barista Audu Bulama Bukarti wanda yake bincike kan harkokin tsaro a cibiyar Tony Blair Institute dake kasar Burtaniya ya bayyana cewa, tsakanin al’ummar Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari sai dai Allah ya isa.

Advertising

Audu Bulama Bukarti wanda gogaggyen Iauya ne dan asalin Jihar Yobe, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a shafin sa na Facebook.

Haka kuma Iauyan ya bayyana cewa: Muddin al’ummar Arewacin Najeriya basu farkar da shugaba Buhari daga baccin da yake ba, to tabbas haka za’a yi ta kashe su shi kuma shugaba Buharin yana ta sharholiyarsa.

Rai da mutunci da dukiyar musulmi da ‘Yar Musulmi da Dan Musulmi sun zama ba’a bakin komai ba yanzu da a karkashin shugabanci dan Kudu ake mana haka, haka zamu yi meye amfanin na kan da ya ki tsare ranka da mutuncin ka da dukiyar ka a lokacin jahiliyar da ma ba’a yi irin wannan rashin imanin ba.

Advertising

Shi kuma yana can sai yawon banza da wofi yake wanda ba zai amfane mu da komai ba, Allah Ya Isa cewar Barista Audu Bulama Bukarti.

Sannan kuma Iauyan ya bayyana cewa: daga can birnin Landan suna can su na shirye—shiryen matakin da zasu dauka, akan yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi wasarere da rayukan al‘umma musaman yankin Arewacin Najeriya.

Ga masu tambaya da cewa: me zasu iya yi wa zai iya fitowa zanga—zanga ko zaman dirshan Wa zai iya shirya Al—kunutu gobe Jumu’ah? Kowa ya shirya abinda zai iya a inda yake. Muma nan muna tattaunawa akan abinda zamu shirya.

Tuni dai ‘Yan Najeriya suka fara bayyana game da yadda matsalar tsaro ke cigaba da kazanta a Arewacin kasar nan, yayin da ake zaman makokin wasu ‘Yan cirani fiye da 40 da ‘Yan bindiga suka kone su kurmus a kauyen Gidan Bawa dake Jihar Sokoto.

Babu shakka girman matsalar tsaro na cigaba da konawa Jama’a gyada a tafin hannu, kuma hakan yasa fushin Jama’ar yankin Arewacin kasar ya fara bayyana karara.

Yanzu haka dai hankulan mafi yawan mutanen Arewacin Najeriya a tashe yake da alamu kuma an kai su bango, dangane da yadda matsalar ta tsaro ke matukar ci masu tuwo a kwarya.

Barista Audu Bulama Bukarti ya kara da cewa: Wato Buhari da ’yan kanzagin sa ba zasu gane kuskuren su ba sai mulki ya kubuce musu, Yanzu da wanne ido zamu kalli wani shugaba daga Kudu mu nemi ya gyara mana matsalar da namu ya kyale tsawon shekara takwas.

Idan Buhari ya sauka bai gyara yanayin tsaro a Jihar Zamfara da Kaduna da Sokoto da Neja da jaharsa Katsina ba, Bayerabe ne ko Inyamuri zai zo ya gyara mana? Idan Buhari bai damu da ranmu ba wani nene zai zo ya damu da mu.

Wallahi sai mulki ya kubuce zamu gane kurenmu ’Yan kujeru da ‘yan kudaden da ku ko iyayen gidanku ke samu yanzu duk zasu kare nan da ’yan shekaru.


Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button