Labarai

Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky Mabiya Shi’a sun fito zanga-zanga domin nuna rashin amincewar su kan ta’addancin dake faruwa a Arewa

Kamar yadda a kwanan nan labarai suka fara karade kafafan sada zumunta kan cewa, zuwa ranar goma sha biyar ga wannan watan da muke ciki Jama’a zasu fito domin yin zanga-zanga akan matsalar rashin tsaro da take addabar al’ummar Arewa.

Baya ga haka ‘Yan kwanakin nan da muke ciki al’amarin ‘Yan Bindiga sai kara ta’azzara yake, inda suka mai da rayukan Jama’a kamar na kiyashi suna ta kaiwa farmaki tare da kashe al’ummar da basu ji basu gani ba.

A yau kuma mun sami wani labari akan Mutanen Zakzaky mabiya Shi’a inda suma suka goyi bayan al’ummar dake shirin fitowa zanga-zanga domin a kawo karshen ta’addanci a Arewacin Nageriya.

Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky mabiya Shi’a mazauna Jihar Sokoto suma sun bi sahun ‘Yan uwan su ‘Yan Arewacin Nageriya, sun fito muzaharar bayyana ra’ayin su tare da kiran gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi Kasar Nageriya musamman Arewa.

Malamin mabiya shi’ar mai suna Sidi Munnir ya bayyana cewa, sun fito wannan gangami ne domin nuna rashin amincewar su kan abubuwan da suke faruwa a Arewacin Nageriya.

Ya kara da cewa: Ana kashe-kashen al’ummar Musulmai babu gaira babu dalili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button