Advertising
Advertising
Labarai

Yadda rayuwar Rahama Haruna ta kare a cikin Bahon roba bayan tasha fama da jinyar da ba’a san irin ta ba har Allah ya karbi rayuwar ta

Rahama Haruna ‘Yar asalin Jihar Kano dake Arewacin Nageriya wanda yake da shekaru goma sha tara 19 wanda labarin ta ya karade ko ina, tunda wani mai daukar hoto mai suna Sani maigatanga ya dauki hotunan ta.

Advertising

An haifi Rahma Haruna tsakanin 1996 zuwa 1997 a Jihar Kano Najeriya tana da shekara shida kafafuwan Rahama da kuma hannayen ta suka daina girma.

Rahama ta kamu da Wata cuta da ba a san irinta ba wanda yasa tanakasa, bata iya yin ayyukan yau da kullun kamar tafiya, rarrafe ko ma sarrafa yawancin kayayyaki.

Sai dai Rahama ta cigaba da zama a cikin bahon roba jim kadan bayan hoton Rahama ya fara yaduwa a Duniya, sai wani Mutumi da ba a bayyana sunan sa ba ya bata kyautar keken guragu don saukaka jigila da ita.

Advertising

lyayen Rahama sun tabbatar da cewa: Sun kashe kusan Naira miliyan daya 1 domin nema mata lafiya amma abin yaci tura.

Bayan nan Rahama ta rasu ne a ranar 25 ga Disamba 2016 tana da shekaru goma sha tara 19 a Jihqr Kano dake Arewacin Najeriya, ta rasu ta bar iyayenta da ‘yan uwanta. Daga B Salia Sicey.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button