Gawurcaccan Dan Bindiga Bello Turji ya tisaltawa magidanta a Jihar Zamfara fita nemo kudin haraji ko kuma suyi ta ran su
Shahararran Dan Bindigar nan wanda ya addabi al’ummar Jihar Zamfara mai suna Bello Turji ya takurawa magidanta yin bilaguro zuwa babban Birnin tarayya Abuja, domin nemo masa kudaden harajin da yake karba a wajan su ko kuma ya aika su lashira.
Daga cikin magidantan da aka sakaya sunan sa ya shaidawa RFI Hausa cewa, Dan Bindigar Turji ya yankewa kauyen s harajin naira Miliyan goma sha bakwai 17 da ya bukaci su biya cikin mako guda kafin zuwa makwanni biyu 2 ko kuma su fuskanci bacin rai.
Nan na nan Mutumin ya nufi babban Birnin tarayya Abuja domin neman kudaden da zai biya harajin da aka gindaya masa, na naira dubu goma sha daya 11 domin tsira da ran sa da kuma na iyalan sa kamar yadda ya shaidawa manema labarai.
Sannan kuma Mutumin ya fadi cewa: Dan Bindigar Turji yayi zirga-zirga cikin tunkaho da jiji da kai a tsakanin al’umma tare da magoya bayan sa, inda har yake zuwa Masallacin Juma’a domin yin Sallah ba tare da yayi wata fargaba ba.
Har yanzu dai ‘Yan Bindigar suna cigaba da kai hare-harega wasu al’ummar dake Arewa maso yammacin Nageriya, musamman Jihar Sokoto da Zamfara wanda a yanzu haka sun fi fama da hare-haren ‘yan ta’adda.
Sannan kuma har yanzu al’ummar Kasar Nageriya suna cigaba da bayyana bacin ran su kan yadda Gwamnatin Kasar ta kasa yin komai wajan shawo kan wannan matsalar tsaron da ta’addancin dake kara tsamari.