Advertising
Advertising
Labarai

Sai da kuka ga uwar bari aka caccakeku a yanar gizo sannan zaku tura tawagar banza domin tsaro, martanin Salihu Tanko Yakasai

Har yanzu dai ana cigaba da cece-kuce da maganganu badan daban akan abin dake faruwa a Arewacin Nageriya kan kashe-kashen al’ummar da ‘yan ta’adda suke a wani sashe a jigar Sokoto.

Advertising

Tun a lokacin da aka kune wasu mutane guda 42 da biyu a Jihar Sokoto Shugaban Kasa Muhammad Buhari da sauran shugabanni suke shan maganganu kala-kala.

To a yanzu ma dai Salihu Tanko Yakasai wanda ake masa lakabi da “Dawisu” yayi wani martani akan Shugaba Buhari akan dai abin da yake faruwa a Jihar Sokoto, bayan da aka tura Jami’an tsaro domin gudanar da tsaro.

Inda Salihu Tanko Yakasai Dawisu yake martanin sa da cewa.

Advertising

Sai da ka ga uwar bari! Sai da ka sha caccaka a yanar gizo. Kai komai baza ka yi dan ƙashin kan ka ba sai an caccake ka! Tawagar ma ta banza ta wofi, su hau jirgi su sauka a karɓe su a fadar gwamnati su sha shayi su koma Abuja, kafin a sake kashe wasu. Aikin kenan dai! Tirrr!.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button