Shugaba Buhari yana kira ga Malami domin aje a masa nasiha tare da fada masa kuskuren abin da yake aikatawa
Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya yi kira ga dukkan Malamai da suje su yi masa nasiha sannan kuma su sanar da shi kuskuren sa, a dukkan lokacin da bukatar hakan ta taso.
A cikin wani faifai bidiyo da yake yawo a kafafan sada zumunta an ga Shahararran Malamin addinin Sheikh Haruna Kabiru Gombe yana yana fadin damar da shugaba Muhammad Buhari ya bawa Malami.
Domin suna zuwa har cikin fadar sa domin suna yi masa wa’azi tare da yi masa nasiha akan abin da ba dai-dai ba ne domin ya gyara.
Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya kara da cewa duk wani lokaci shugaba Bubari yana basu dama domin suje har cikin Fadar sa, domin a sanar da shi a ina kuskuren sa yake.
Malamin ya kara da cewa: Haramun ne shugaba ya bada damar ayi masa nasiha sannan a nuna masa kura kuran sa, amma azo ana zagin da bisa kan manbari.
Domin kuji cikekken bayanin da Sheikh Kabiru Haruna Gombe yake akan kiran da shugaba Buhari ya musu domin suna masa wa’azi da nasiha, sai ku danna shudin rubutun dake kasa.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇