Advertising
Advertising
Labarai

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Bafarawa yayi martani ga Shugaba Buhari har da cewa Buhari yaji tsoron haduwar sa da Allah

Kamar yadda kuka sani a yanzu haka al’amarin kashe kashen al’umma da ‘Yan Bindiga suke yi ya ta’azzara a Arewacin Nageriya musamman Nigar Sokoto, inda a kwanan nan an kashe al’ummar cikin Jihar da dama.

Advertising

To a yau kuma tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana takaicin sa akan kisan kiyashin da ‘Yan Bindiga suke wa al’ummar Jihar Sokoto, inda yake kira ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari da yaji tsoron haduwar sa da Allah.

Tsohon Gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake shira da gidan jaridar BBC Hausa, tsohon Gwamnan ya fadi hakan ne akan abin da ‘Yan Bindiga suka aikata ga wasu Mutane da suka kone a cikin Motar Bas dake karamar hukumar sabon Birni a Jihar Sokoto.

Tsohon Gwamnan ya kara da cewa: Wajini ne shugaba Buhari yabi al’umma ayi zama na musamman domin tattaunawa, kamar yadda yabi Mutane gida-gida lokacin da yake neman kuri’a sabida mu taimaka masa wajan haduwar sa da Allah.

Advertising

Sannan kuma hare-haren masu garkuwa da mutane yana cigaba da haddasa mutuwar al’umma a yankin Arewa maso yammacin Nageriya.

lamarin hare-haren yafi tsamari a yankun sabon Birni da kuma Isah dake Jihar Sokoto, da kuma yankin shinkafi dake Jihar Zamfara duk da Gwamnatin tarayya da ta Jihohi suke cewa sun yi.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button