Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Tsohuwar Jaruma Fati Muhammad ta bayyana dalilin da yasa ta dawo Masana’antar Kannywood domin ta cigaba da harkar Fim a yanzu

Tsohuwar Jarumar Masana’antar Kannywood Fati Muhammad wanda tayi sharafin ta a shekarun baya wanda ta dauki tsawon shekaru masu yawa ba’a sake jin duriyar ta ba a Masana’antar.

Advertising

Jaruma Fati Muhammad ta bayyana cewa: Dalilin da yasa ta dawo cigaba da harkar Fim shine sabida masiyanta sun sha kiran ta akan cewa da dawo Masana’antar, amma sai yanzu ta amsa kiran da suke mata inda hakan yasa masoyan nata jin dadi matuka.

An tambayi Jaruma Fati Muhammad cewa: Ko mai ya ja hankalin ta har ta dawo Masana’antar Kannywood domin ta cigaba da harkar Fim a yanzu, sai ta bayyana cewa.

Dalilin shi ne nayi shawara da Ali Nuhu kuma ya bani kwarin gwiwa sosai wanda a yanzu haka zai shirya sabon Fim wanda zan fito a cikin sa, kuma a yanzu ma ana daukar Gidan Danja da ni zango na biyu 2.

Advertising

Bayan nan an sake tambayar Fati Muhammad da cewa: Shin ya taji lokacin da ake yada hoton ta kan cewa ta tsufa, sai ta sake fadin cewa.

Alhamdulillah tun da har Allah yasa na sami tsawon rai dana tsufa domin tsufa dolene ga kowa idan har yayi tsawon rai, kuma hotunan da ake magana a kai na cewa na tsufa nayi kwalliya ne sai na shiga taro sai kwalliyar ta cabe, sabida haka ko kadan banji haushin maganar da ake fada ba kan wannan hotunan.

Wannan ita ce shirar da aka yi da tsohuwar Jaruma Fati Muhammad akan dawowar ta harkar Fim a yanzu, da kuma maganganun da Mutane sukayi akan wasu hotunan ta wanda ake cece-kuce da cewa ta tsufa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button