Advertising
Advertising
Labarai

Ina kira ga Gwamnati ta farga akan ta’addanci da zaluncin da ake mana mu ‘Yan Arewa, cewar Sheikh Dr Sani Umar Bichi

Shugaban Malamai Na jibwis NHQ jos Kano state sheikh Dr Sani sharif Umar Bichi yace, Shugaban kasa yayi rauni ya kara karfi a gwamnatin sa ana cutar damu yan Arewa ta hanyar kashe mu da zalintar mu tabargare kala-kala ba gaira ba dalili don haka muna Kira ga gwamnati ta farga.

Advertising

Sannan Malamin ya kara da cewa: Talakawa ba zagin shugaban kasa ba kona Dss da kona ‘Yan Sanda kona sojoji ba fa shine agabanmu ba, muyi musu addu’a ko Allah zeji kanmu su gyara kuma Shugaban kasa mun masa kyakkyawan zato muka zabe shi kuma asanda muka zabe shi mutum ne me amana.

Amma a yanzu yayi rauni kuma ina kira ga Shugaban kasa wanda yabaka shawara akan kara farashin man fetur wallahi makiyin ka ne, idan kuma ance sai an dauka muna addu’a Allah Ya lalata wannan shiri ya lalata wannan mutum.

Mallam yakara da cewa: Shugaban kasa kayi rauni yakamata kakara karfi a yanzu wannan gwamnatin kaso dari 100% Na aikin da ya kamata ayi befi kaso 30% aka yiba duk wanda yayi ba dai-dai ba anuna masa yayi kuskure duk wanda baze iya ba a cireshi asa wanda zai iya.

Advertising

Sannan kuma Malamin yace: Ya kamata Buhari da ministocin sa da sauran su suji tsoron gamuwarsu da Allah kar su manta saura shekara daya subar mulki, ya kamata subar abinda za’a dinga kallo ana shi musu Albarka kamar yanda sardauna da tabawa balewa suka yi.

kuma Ina bawa gwamnati shawara takarawa bodojin Nageriya tsaro sabida ta’addancin da ake yi a Jihar Sokoto da katsina, Dan Nageriya ba zai yiwa dan uwan sa haka ba don haka dole asawa bodoji ido akara musu tsaro.

Mallamin yace: An cutar da Arewa ta hanyar lalata matasan mu da shaye-shaye da kin basu aikin yi don haka dole yahudawa komai sukai musu tayi zasu Shiga, su kuma mata yada tsiraici a social media kamar
TIKTOK kunga dole Allah ya jarabce mu da abubuwa kala-kala.

Mallamin ya yi wannan bayani ne a muhadarar daya shirya mai taken Abubuwan da suke faruwa a Nageriya na zalunci da kashe-kahse a Arewa.

A karshe Mallamin yayi addu’o’in zaman lafiya ga Arewa dama Nageriya baki daya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button