Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Masu garkuwa da Mutane sun tare Mahaifiyar Jaruma Samha Nura M Inuwa akan hanyar Kaduna zuwa Kano

Innalillahi wa inna ilaishi raji’u: Mahaifiyar Jaruma Samha Nura M Inuwa ta hafu da masu garkuwa da Mutane akan hanyar Kaduna.

Advertising

Har yanzu dai tsaro da firgici da tashin hankali suna kara hauhawa a zukatan al’ummar Nageriya, musamman ma bangaren Arewacin Kasar.

A daren jiya ne dai masu garkuwa da Mutane akan hanyar Kaduna suka tare Mutane ciki har da Mahaifiyar daya daga cikin Masana’antar Kannywood, wato Jaruma Samha Nura M Inuwa.

Kuma masu garkuwa da Mutanen sun tare su ne a lokacin da suke kokarin shiga Kaduna daga Jihar Kano.

Advertising

Jaruma Samha ta wallafa wannan magana ne akan shafin ta na TikTok inda take kuka take neman addu’ar ‘Yan uwa da abokan arziki, akan abin da ya faru da Mahaifiyar ta.

Samha ta bayyana cewa: A lokacin da masu garkuwar da Mutanen suka tare Motar da Mahaifiyar ta take ciki sai Mutanen cikin Motar suka fito a dimauce, inda suka ruga da gudu cikin Daji amma abin da faru ne a cikin dare.

To a dai wannan lokacin ne sai mahaifiyar Samha ta kira waya ta sanar da halin da suke ciki a cikin takar Dajin, wato irin inda Bahaushe yake cewa ba gida gaba ba gida baya.

Domin kuji cikekken labarin sai ku kalli bidiyon da muka saka muku a kasa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button