Advertising
Advertising
Labarai

Mun gama dukkanin shirye shiryen kawo karshen hare haren ‘Yan ta’adda a Arewacin Najeriya na har abada, cewar Shugaba Buhari

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa: Sun gama dukkanin shirye—shiryen kawo karshen hare-haren ta’addanci a Arewacin Najeriya na har
abada~Buhari.

Advertising

Mai baiwa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan yada labarai “Malam Garba Shehu” ya shaida wa BBC Hausa cewa, za’a hada hannu da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen kasar Nageriya domin kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na har abada.

A yau Lahadi aka soma taron shugabanin kungiyar “ECOWAS” ko kuma “CEDEAO” karo na shittin 60 a Abuja, Wannan taro zai gudana ne a daidai lokacin da yawancin kasashen yammacin Afrika ke cikin wani yanayi na tsananin rashin tsaro, duba da yadda kungiyoyin tayar da kayar baya da sauran ‘Yan Bindiga suka addabe su.

A ‘yan kwanakin nan mahara sun kona matafiya sama da 42 a Jihar Sokoto dake Arewacin Nageriya, kuma kafin nan wasu maharan sun kona wasu matafiyan dake hanyar su ta zuwa kasuwa a Mali.

Advertising

Garba Shehu ya bayyana cewa: Shugaban kasa ya tura wakilci na musamman na masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaron kasa musamman domin samar da bayanan sirri, kuma sun je sun tattauna da wakilai a matakin kananan hukumomi da Jihohi sun dawo masa da rahoto kuma za’a ga abin da zai biyo baya.

Haka zalika ya kara da cewa: A matakin kasa da kasa taron na “ECOWAS” ko kuma “CEDEAO” zai ba da tasa gudummuwa wurin kawo karshen hare-hare a Arewacin Najeriyar.

Wannan batu yana daya daga cikin ajanda da Shugabanni zasu tattauna Abu ne da ya damu kowa, kuma babu wani Shugaban kasa da za’a ce hankalin sa ya kwanta da wannan fitina da ake fama da ita.

Garba Shehu yace: Saboda haka za’a dauki mataki nan ba da jimawa ba sannan za’a kawo karshen hare-hare a Arewacin Najeriya na din-din-din.

Bayan haka Hukumomi da Jihohi sun dawo masa da rahoto kuma inda za’a ga abin da zai biyo baya haka zalika yace, a matakin kasa da kasa taron na “ECOWAS” ko kuma “CEDEAO” zai ba da tasa gudummuwa wurin kawo karshen hare-hare a Arewacin Najeriyar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button