Advertising
Advertising
Labarai

Kotu ta bada umarnin aika wani matashi mai shekaru 37 gidan yari kan wani babban laifi da ya aikata

Kotu ta bada umarnin aika wani matashi mai shekaru 37 gidan yari kan wani babban laifi da ya aikata

Kotun Shari’ar Muslunci ta aike da wai mutum mai suna Yusha’u Ado zuwa gidan yari bisa zargin satar katan 22 na maggi.

Advertising

A yau ne a ka gurfanar da Ado a gaban kotun
bisa laifuka biyu da suka hada da cin amana
da kuma cuta, inda ya kuma amsa laifukan bayan an karanto masa su.

Dan sanda mai kara Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa, wani mai suna Jamilu Ibrahim, mazaunin unguwar Galandanci ne ya kawo korafin a caji ofis na Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Rubutaccen bayanan karar yace, Ibrahim ya baiwa Ado ajiyar kayan din maggi 260 ya ajiye masa, amma da ya zo karba sai gano cewa babu kwalaye 22 na maggin, wanda kudin sa ya kai naira dubu 261.

Advertising

Bayan ya gama jin karar, alkalin kotun Dakta
Bello Khalid ya bada umarnin mayar da mai laifin gidan yari sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button