Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Saratu Daso ta bayyana cikin bidiyo tana kokawa tana kira ga shugabanni da su tashi su kawo karshen ta’addanci a Arewa

Kamar yadda kuka sani har yanzu dai al’ummar Kasar Nageriya suna cigaba da fadin maganganu kala-kala akan matsalar tsaron Kasa, da kuma kashe-kashen Mutanen da ake da basu ji basu gani ba.

Advertising

Wanda har a yau ma Jarumar Masana’antar Kannywood suna sake bayyana a cikin bidiyo da suke wallafawa a shafukan su na sada zumunta, inda suke nuna alhinin su kan abubuwan da suke faruwa a Arewacin Kasar Nageriya.

To a yau ma dai Jarumar Masana’antar Kannywoos Saratu Daso wacce ake mata lakabi da Mama Daso, ta bayyana cikin wata bidiyo wanda ta wallafa a shafin ta na sada zumunta Instagram.

Inda ta cikin bacin rai da harzuka tana mai nuna alhini da kokawa akan cin zali da kisan kiyashin da ake wa al’ummar, Arewa musamman al’ummar Jihar Sokoto da kuma Zamfara.

Advertising

A cikin bidiyon Mama Daso tana kira ga Gwamnatin tarayya da kuma Gwamnatin Jiha akan su tashi tsaye wajen kawo karshen ta’addacin cin da ake a Kasar Nageriya musammam ma Arewacin Kasar.

Sannan take cewa: Wannan abin da yake faruwa ya ishe mu, ya ishe muya ishe mu, ya kamata shugabanni su yi wani abu a kai.

Domin kuji cikekken bayani daga bakin Jaruma Saratu Daso wacce aka fi sani da Mama Daso akan kashe-kashe Mutamen da ake a Arewa da kuma matsalar tsaro, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

https://www.instagram.com/p/CXTy-zNDyrr/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button