Labarai
Yanzu-yanzu: Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya dawo daga kwas din koyon dabarun mulki
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya dawo daga kwas din koyon dabarun mulki.
Advertising
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nmandi Azikiwe dake babban birnin tarayya Abuja.
Bayan shafe tsawon mako guda a wata makaranta mai suna Harvard Business School, a birnin Boston dake America inda yaje domin samin horo akan dabarun mulki.
Advertising
A makon jiya ne kwamishinan yada labarai na Jihar Kano kwamared Muhammad Garba ya bayyana cewa.
Gwamna Ganduje ya mika ragamar shugabancin Jihar a hannun mataimakin sa Nasiru Yusuf Gawuna, kuma dukkan masu mukaman gwamnati zasu yi aiki da mataimakin nasa ne idan bukatar hakan ta taso.
Nasara Radio 98.5 FM.
Advertising