Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mu ‘yan Fim ba jahilai bane muna da ilimin mu domin muna fadakarwa a shirin Fina-Finan mu, inji Jaruma Ummi Abdulwahab

Ummi Abdulwahab wacce Jaruma ce a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood wanda wasu sun fi sanin ta da Ummi El-Abdul, ta bayyana cewa su ‘Yan Fim ba jahilai bane domin suna da ilimin su dai-dai gwargwado shi yasa ma suke fadakarwa a harkar su ta Fim.

Advertising

Jaruma Ummi Abdulwahab ta bayyana hakan ne a lokacin da suke shira da wakilin Jaridar Damukaradiyya, akan Mutanen da suke musu kallon cewa basu da ilimi shi yasa suke aikata abin da sukaga dama.

Jarumi Ummi ta kara da cewa: Ai shi ilimi baya buya domin ana ganin sa a cikin sana’ar da muke yi don haka mu ba jahilai bane muna da ilimi, sabida haka a daina mana kallon marasa ilimi.

Ummi Abdulwahab ta kara da cewa: Kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwar sa don haka muna haka rayuwar mu ta kasan ce, kuma yanzu da nake harkar Fim idan Allah ya kawo min Miji tayi aure shikenan sai dai a rinka labarin na taba yin harkar Fim a baya.

Advertising

Daga karshe Jaruma Ummi Abdulwahab tayi addu’ar Allah yasa ta gama harkar Fim lafiya, sannan kuma ta sami Mijin aure.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button